Chadi: An kama mai shirya gangamin adawa da Deby

Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaba Idris Deby na son tsayawa takara karo na biyar

Jami'an tsaro a Chadi sun kama wani mai fafutuka wanda ya shirya gangamin nuna adawa da shugaban kasar Idriss Deby.

Wannan gangamin dai shi ne wanda mutane suka yi ta hura usur daga gidajensu a baya-bayan nan, domin nuna bukatar shugaban ya sauka daga mukaminsa.

An tsare mutumin ne mai suna Mahamat Nour Ibedou, wanda shi ne kakakin kungiyar fararen hula ta Ca Suffit, sakamakon shirya gangamin adawa da shugaba Deby wanda zai tsaya takara a karo na biyar a zabukan da za a gudanar a watan gobe.

A shekara ta 1990 ne shugaba Idriss Deby ya dare kujerar shugabancin kasar.

Mista Ibedou ya ce a wani mataki da hukumomin Chadin suka dauka na ganin gangamin hura usur din bai yi nasara ba, hukumomin sun bi duk sun saye usur din da ke kasuwannin kasar.

Karin bayani