Congo: Sassou na hanyar lashe zabe

Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaba Sassou Nguesso

Sakamako na farko da Hukumar zabe ta kasar Congo Brazzaville ta bayyana ya nuna cewa Shugaban kasar Congo, Denis Sassou Nguesso shine yake kan gaba wurin lashe zaben shugaban kasa da aka yi ranar lahadi a kasar.

Bisa ga kuri'un da Hukumar ta kidaya, Denis Sassou Nguesso ya samu kashi 67 na kuri'un da aka kada.

Sa'annan kuma Guy Brice Parfait Kolelas ne yake biye da shi da kashi 16.

A yayin da kuma Jean Marie Michel Mokoko ya zo a na 3 da kashi 7.

Sai dai a yanzu haka tuni 'yan takarar jam'iyun adawa suka fara yin korafi game da wannan sakamakon zaben da 'yan takara 9 suka fafata. Denis Sassou Nguesso mai shekaru 72 a duniya ya debi shekaru 32 yana kan kujerar mulki.