Ebola ta sake bulla a Guinea

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mutane hudu sun mutu sakamakon kamuwa da cutar ebola a Guinea

Hukumomin kiwon lafiya a kasar Guinea sun ce sun gano wasu daruruwan mutane wadanda mai yiwuwa suka yi mu'amala da wasu da suka kamu da kwayar cutar Ebola bayan da aka sake samun bullar cutar da ta hallaka mutane 4 a kudu masu gabashin kasar.

Wani kakakin cibiyar da ke kula da yaduwar cutar, Fode Tass Sylla ya ce sun gano mutane 816 daga iyalai 117 tun a ranar asabar.

Ya kara da cewa za'a killace mutanen har na tsawon makonni uku.

Fiye da mutane dubu goma sha daya suka mutu sakamakon bullar cutar a kasashen Guinea, da Liberia da kuma Sierra Leone tun daga karshen shekarar 2013.