An kai hari wani Otel a Mali

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An kashe dan bindiga guda a cikin maharan

Wasu 'yan bindiga sun kai hari a wani otel da jami'an soji na tarayyar turai suka sauka a Bamako babban birnin kasar Mali.

Ministan tsaron kasar Malin ya ce an hallaka daya daga cikin 'yan bindigan a musayar wuta da suka yi da masu gadi a wajen, yayin da kuma aka kama wasu mutane biyu da ake zargi da hannun su.

An dai samu musayar wuta a tsakanin 'yan bindigar da kuma jami'an tsaro. Duk da kasancewa akwai cikakken tsaro a otal din da akai harin, 'yan bindigar sun samu nasarar kai harin wajen.

Otal din mai suna Nord-Sud Azalai an mayar da shi wajen shalkwatar da jami'an soji na tarayyar turai suka sauka domin horar da ma'aikatan tsaron Mali.

Jami'an tarayyar turan da aka turo don horas da ma'aikatan tsaron Mali sun tabbtar da cewa ba bu daya daga cikin su da aka jiwa rauni.

A watan Nuwamba ne wa su mayaka dake da alaka da kungiyar Al-Qaeda suka kai hari a otel din Radisson Blu dake kusa da wurin.

Tuni aka tura jami'an tsaro da dama zuwa otal din domin tabbatar da tsaron rayukan wadanda ke ciki.Kuma har yanzu ba bu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin.