Nigeria: Shi'a ta kai gwamnati kotun ICC

Image caption Mabiyan Elzakzaky sun dade suna neman da a saki shugaban nasu.

Kungiyar mabiya mazhabar shi'a a Najeriya ta ce ta kai gwamnatin Najeriya kara kotun masu aikata miyagun laifufuka ta duniya ICC, bisa arangamar da 'ya'yan kungiyar suka yi da sojojin kasar.

Kungiyar ta ce ba ta ji dadin yadda kwamitin da gwamnatin ta kafa yake tafiyar da bincike ba, a kan kisan gillar da take zargin sojoji sun yi wa dimbin magoya bayanta, a Zaria, lokacin da sojojin suka zargi 'yan shi'a da yunkurin kashe babban hafsan sojoji.

A karo da dama, an sha dage zaman hukumar binciken, bisa dalilin dagewar da lauyoyin kungiyar suka yi, cewa sai sun gana da jagoran kungiyar, Sheikh Ibrahim Elzakzaky da ke tsare, kafin su bada hadin kai ga hukumar binciken.

Wannan rikici na Shi'a da sojoji dai ya jawo ce-ce-ku-ce a Najeriya da ma wasu kasashen duniya kamar su Iran da ke marawa 'yan shi'ar baya.