Obama ya kammala ziyararsa na Cuba

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaba Obama ya ce kasar sa baza ta tilasta wa Cuban aiwatar da sauye-sauye ba.

Ranar Talata ce ranar karshe ta ziyara mai cike da tarihi da Shugaban Amurka Barack Obama yake yi a Cuba.

Shugaba Obaman ya ce ya je Cuban ne domin kammala sasanta rashin jituwan da yayi ke tsakanin kasar da Amurka, tun daga lokacin yakin cacar-baka.

A jawabin daya gabatar wanda gidan talabijin na Cuban ya nuna, Mista Obama ya ce lokaci ya yi da za a samu sauyin dangantaka tsakanin Amurka da Cuba.

Ya buka ci jama'ar Cuba da ta rungumi sauyi, sannan ta dubi gaba da fata na gari.

Mista Obama ya ce Amurka za ta mutunta banbance-banbance da ke tsakanin kasashen biyu, kuma ba za ta tilasta wa Cuban aiwatar da sauye-sauye ba.

Shugaba Obama da takwaransa na Cuban Raul Castro sun yi shiru na minti daya don nuna jimamin mutanen da suka mutu a hare-haren da aka kai Brussels.