'Shigo da shinkafa Nigeria haramun ne'

Image caption Nigeria dai ta kasance mai albarkatun kasa da za a iya noma shinkafa.

Hukumar hana fasa-kwauri ta Najeriya ta ce sakamakon gano kudin shigarta bai kai yadda ake bukata ba saboda fasakwaurin shinkafa da ake yi, ta sake haramta shiga da shinkifa kasar ta iyakokin da ba na ruwa ba.

A watan Oktoban bara ne dai hukumar ta ba da damar shiga da shinkafar muddin za a biya kudin fito kamar yadda ya dace.

Sai dai, a cewar hukumar, da farko kwalliya tana biyan kudin sabulu amma daga watan Janairun bana zuwa yanzu kudin shigar da ta samu naira biliyan daya da miliyan dari shida da tamanin bai kai abin da ya kamata a ce ta samu ba, don haka take zargin ana fasa kwaurin shinkafar.

Kakakin hukumar hana fasa-kwauri ta Najeriya Wale Adeniyi ya shaidawa BBC ce wa a watan Oktobar shekarar da ta gabata ne aka amince a shigo da shinkafa ta iyakokin kasar, amma a yanzu an soke wannan shawara.

Hakan na nufin an haramta shigo da ita ta iyakokin kasa da kuma ta tashoshin jiragen ruwa, an dauki matakin ne saboda an samu rahoton an shigo da shinkafa ta tasahr jirgin ruwa da ke Kwatano amma kuma ba a samu kudaden shigar da su suka kai yawan abinda aka shigo da su ba.