Amurka da Biritaniya sun yi tir da zaben Rivers

Hakkin mallakar hoto Channels TV
Image caption Hukumar zaben Najeriya ta koka kan yadda aka sace mata jami'ai a jihar Rivers lokacin zaben

Gwamnatocin Amurka da Biritaniya sun yi Allah-wa-dai da munanan abubuwan da suka faru a lokacin gudanar da zaben zagaye na biyu a jihar Rivers da ke kudancin Najeriya.

'Yan Biritaniya masu sa ido a zaben sun ce sun ga yadda aka gudanar da al'amura ba bisa ka'ida ba a wajen kada kuri'a da kuma yadda mutane da dama basu fito zaben ba saboda tsoron barkewar rikici.

A sanarwar da ofisoshin jakadancin kasashen biyu da ke Najeriya suka fitar, sun yi kira ga shugabannin jam'iyyun da su ja kunnen magoya bayansu tare da bin doka da oda.

Kazalika sun yi tir da sace ma'aikatan hukumar zabe da aka yi a jihar.

A ranar Asabar din da ta gabata ne aka yi zaben a jihar Rivers, wanda hukumar zabe ta dakatar da zabukan da aka yi a kananan hukumomi takwas saboda kashe-kashen da aka yi da kuma sace mata ma'aikata.

Karin bayani