Al-Shabab ta haramta sayar da kayan Turkiyya a Somalia

Rahotannin da aka samu daga shafin intanet na Falaar, da ke goyon bayan Al-shabab na cewa kungiyar ta bai wa 'yan kasuwa da ke yankin Shabelle a kudancin Somaliya, umarnin cewa su daina sayan kayan da aka kawo daga kasar Turkiyya.

Kungiyar ta Al-Shabab ta yi wa al'ummar da ke zaune a garin gargadin cewa za a kone a raye, duk wani dan kasuwar da aka gani yana mu'amala da kayan Turkiyya.

Wasu 'yan kasuwa a yankin sun nuna damuwar su game da haramcin, inda suka ce zai bata musu harkokin su na kasuwanci.

Kungiyar ta zargi Turkiyya da goyon bayan gwamnatin Somaliyar wadda Al-Shabab din ke adawa da ita.

Da farko kungiyar ta ce kayan da ake shigowa dasu daga waje na kashe kasuwar masu kananan jari a kasar.

Turkiyya dai da manyan 'yan kasuwar Turkiyyan na samun riba sosai a Somaliya, musamman a Mogadishu babban birnin kasar.