'Yan BH na mika wuya ga sojoji

Hakkin mallakar hoto Nigeria Army
Image caption Sojojin Najeriya dai na ci gaba da kokarin kakkabe mayakan Boko Haram

Rundunar sojin Najeriya ta ce tana ci gaba da samun nasara a kan 'yan kungiyar Boko Haram a yankin arewa maso gabashin kasar, inda wasu mayakan a yanzu ke mika wuya ga sojojin kasar.

Kakakin runduna ta musamman da ke yaki da kungiyar ta Boko Haram da ake kira operation Lafiya Dole, Kanar Mustapha Anka ne ya bayyana hakan a wata hira da suka yi da BBC.

Kanar Anka ya ce dakaru na ci gaba da kama mayakan Boko Haram da kuma kakkabe maboyarsu.

Ya kara da cewa babban hafsan sojin Laftanal Janar ya sake kaddamar da wata runduna da za ta yi nata aikin a yankin Munguno da Baga da Damasak don kara gano mayakan.

Kanal Anka ya kuma ce a yanzu haka yunwa da wahala na sa mayakan kungiyar suna kawo kansu ga sojojin, sakamakon kewaye su da aka yi ta sama da ta kasa.

Ga dai yadda hirar tasu ta kasance da Bashir Sa'ad Abdullahi, lokacin da suka kai ziyarar aiki garin Dikwa na jihar Borno,inda ya fara ne da bayyana halin da ake ciki yanzu game da yaki da kungiyar ta Boko Haram:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti