Chad: Amnesty na neman sakin wasu mutane

Image caption masu neman ficewar Deby akan mulki

Kungiyar Amnesty International ta nemi ga gwamnatin kasar Chadi da ta saki wasu mutane 2 da take zargi da neman tada zaune tsaye.

Mahamat Nour Ibedou da kuma Nadjo Kaina Palmer wadanda jigogi ne na wasu kungiyoyin fararen hula sun gurfana a gaban jami'an tsaro na 'yan sanda suna amsa wasu tambayoyi.

Samira Daoud ta Amnesty tace, kama wadannan mutane, wata alama ce na nuna take hakkokin bani Adam makwanni 3 gabannin zaben shugaban kasa.