Dan China ya amsa satar bayanan Amurka

Hakkin mallakar hoto

Wani dan kasar China mai shekaru hamsin ya amsa cewar, yana da hannu a kokarin satar bayanan sirri na tsaro na sojan Amurka.

Shi dai Su Bin, dan shekaru hamsin, yana cikin wani gungu ne na masu kokarin satar bayanan sojan Amurka da suka shafi jiragen yaki, da jiragen sama na dakon kaya, da kuma wasu makamai.

Ma'aikatar shari'a ta Amurka ta sanar da cewa shi Mista Su ya shiga wannan harka ce domin samun kudi.

An dai kama shi ne yayin da yake aiki a Canada cikin shekara ta 2014, kuma yanzu yana fuskantar daurin shekaru biyar da kuma tarar dalar Amurka 250,000.

Sai dai wannan ba shi ne karon farko ba da Amurka ke zargin masu alaka da China da kokarin satar bayanan sirri.