Matsalar mai ta kusan zuwa karshe

Dr Ibe Kachikwu. Hakkin mallakar hoto NNPC
Image caption An dade ana fama da karancin Man Fetur a Najeriya.

A Najeriya kamfanin mai na kasar NNPC ya yi tabbatar da cewa zai yi bakin kokarin sa wajen tabbatar da Man fetur ya wadata a kasar cikin makwanni masu zuwa dan kawo karshen dogayen layukan da ake fama da su a gidajen Mai a wasu sassan kasar sakamakon karancin da ya yi.

A wata sanarwa da kamfanin ya fitar, ya ce karamin Ministan mai kuma shugaban hukumar NNPC Dr Ibe Kachikwu ya bada umarnin a tabbatar da an rarraba mai yadda ya kamata dan ya wadata.

Dr Ibe Kachicku ya yi wannan jawabi ne ya yin wata ganawa da shugaba Muhammadu Buhari da kungiyoyin kwadago a fannin mai wato PENGASSAN da NUPENG dan tattaunawa kan batun karancin mai a Najeriya.

Sanarwar da NNPC ya fitar ya kuka da rashin fahimtar da wasu suka yi wa bayanin Dr Ibe Kachikwu na cewa za a ci gaba da fuskantar matsalar mai har zuwa watan Mayun shekarar nan.

Ministan yace su na yin kokarin da za su yi dan kawar da wasu matsaloli da ke kawo cikas ga rarraba mai a duk fadin Najeriya.

Musamman ma ta fuskar batun musayar kudaden waje da ake samarwa dillalan mai wanda minista yace ya na aiki tare da babban bankin kasar CBN domin warware wannan matsalar.