Majalisa ta zartar da kasafin kudin 2016

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A watan Disambar 2015 ne shugaba Buhari ya gabatar da kasafin kudin 2016

Majalisar dattawan Najeriya ta zartar da kasafin kudin shekarar 2016, a ranar Laraba.

Ta kuma yi kira ga gwamnati da ta yi amfani da kasafin kudin wanda ba a taba mai yawa irinsa ba, ta hanyar da ya dace, duba da halin da tattalin arzikin kasar ya shiga sakamakon faduwar farashin man fetur.

A yayin da yake jawabi shugaban majalisar Sanata Bukola Saraki, ya ce, "An karanta wannan kuduri sau uku kenan ana kuma zartar da shi. Yanzu kuma ya rage wa gwamnati ta yi amfani da shi yadda ya dace."

To sai dai 'yan majalisun dokokin sun rage kasafin kudin da kasafin kudin da shugaban kasar ya gabatar masu da kashi 10 cikin 100 wato sun rage kudi kusan naira biliyan 17.

A watan Disamba ne shugaba Muhammadu Buhari ya gabatar da kasafin kudin a gaban majalisa na naira tiriliyan shida da biliyan 77 da miliyan 680, kwatankwacin dala biliyan 30, amma ya nemi da a janye shi bayan wata daya don yin gyare-gyare, sakamakon faduwar farashin man fetur.

Yawan kudin dai bai sauya ba amma gibin kasafin ya karu da naira tiriliyan uku daga naira tirilyan 2.2.

Har yanzu babu tabbacin ta inda za a samu kadaden da za a yi amfani da su wajen kasafin ba duba da yadda kudin da ake samu a baya ta bangaren man fetur wanda da shi Najeriya ta dogara ya ragu, saboda faduwar farashinsa a duniya.