Sojoji sun ceto mutane 180 da Shanunsu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Sojojin Najeriya sun kubutar da mutane da dama daga hannun 'yan kungiyar Boko Haram

A Nigeria a kokarin da sojojin kasar su ke na kakkabe mayakan kungiyar Boko Haram, sun kubutar da mata da maza da kuma kananan yara 180.

An kubutar da su ne a lokacin da suke aikin kakkabe 'yan ta'addar daga kauyukan Menari, da Bulamari, da Zangebe, da Mafa, da Mijigine, da Bale da Kaltaram duk a karamar hukumar Mafa a jihar Borno.

Haka kuma sojojin sun kubutar da garken Shanu guda da mayakan suka sace a kauyukan Galtimari da Bale.

Sojojin sun yi wannan nasara ne da taimakon 'yan kato da gora da aka fi sa ni da Civilian JTF, sun kuma yi nasarar hallaka 'yan Boko Haram biyar ya yin gudanar da aikin.