Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Masu yoyon fitsari na bukatar karin agaji

Image caption Yawancin matan a wajen haihuwa suka kamu da larurar yoyon fitsari.

A Najeriya larurar yowon futsari na daga cututtukan da mata kan hadu da su a lokacin haihuwa.

Larurar dai kan kama mata ne wadanda suka dauki tsawon lokaci suna nakuda, kuma sukan dauki watanni a killace suna karbar magani bayan an yi musu aiki, kafin su koma rayuwa kamar yadda kowa yake yi.

Bangaren kiwon lafiya dai na fuskantar matsaloli da dama ciki kuwa har da rashin kwararrun likitoci da sauran jami'an lafiya.

Wakilin mu Yusuf Ibrahim Yakasai ya ziyarci cibiyar kula da masu yoyon fitsarin dake Kano don ganin ci gaban da aka samu wajen kula da masu lalurar ga kuma rahoton sa.