Nigeria: Rigingimun da ke jam'iyyar APC

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Jam'iyyar APC ce take shugabanci a Najeriya.

Jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya, na fuskantar rigingimun cikin gida, kama daga matakin tarayya da jihohi har ma zauwa kananan hukumomi.

Hakan dai yasa wasu ke ganin cewa jam'iyyar ka iya fuskantar wargajewa.

Ko a makon da ya gabata ma, alamu sun nuna cewa jam'iyyar tana son kecewa zuwa gida uku, a jihar Kano sakamakon wani sabanin da ya shiga tsakanin gwamnan jihar, Abdullahi Ganduje da tsohon gwamna, Rabi'u Musa Kwankwaso.

Irin wannan rikicin ne dai jam'iyyar take fuskanta a jihar Kaduna.

Kawo yanzu dai jam'iyyar ba ta gudanar da zaben shugabannin kwamitin amintattunta ba, ballantana a kaddamar da shi.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan takarar shugabancin kasar a karkashin jam'iyyar lokacin babban taron da APC ta yi a Lagos, Naigeria.

Sai dai kuma sakataren jam'iyyar ta APC na kasa, Alhaji Maimala Buni ya shaidawa BBC cewa nan ba da dadewa ba za a gudanar da zabubbukan.

A daren ranar Talata ne dai jiga-jigan jam'iyyar ta APC suka yi wata ganawa karkashin jagorancin shugaba Muhammadu Buhari. Sai dai kuma har yanzu babu bayani kan abin da aka tattauna.

Masu sharhi na ganin cewa jam'iyyar ta APC ba za ta yi karko ba irin wanda jam'iyyar adawa ta kasar, PDP ta yi wadda ta kwashe shekara 16 tana mulkin kasar.

A ranar 6 ga Fabrairun 2013 ne manyan jam'iyyun adawa guda uku na kasar da suka hada da Action Congress of Nigeria, ACN da Congress for Progressive Change, APC da kuma All Nigeria People's Party, APC.

An kuma samu wasu masu fada a ji a jam'iyya mai mulki a lokacin wato PDP, da suka sauya sheka zuwa jam'iyyar APC.