Nigeria: 'Dole NNPC ya biya gwamnati kudi'

Hakkin mallakar hoto NNPC
Image caption Ministan mai na Najeriya, Ibe Kacikwu

Hukumar tarawa da raba arzikin Najeriya, RMAFAC ta ce bisa bayanan da ke hannuna, kamfanin man fetur na kasar watau NNPC ya ki saka kudi da yawansu ya kai tiriliyan biyar, a cikin asusun gwamnati.

Hukumar ta RMAFAC ta ce a tsawaon shekara biyar, NNPC ba ta zuba kudin a baitil malin gwamnati.

A saboda haka, hukumar ta ce dole ne NNPC ta mayar da kudaden domin haka doka ta tanada.

Wannan dai na zuwa ne kimanin mako guda da ofishin babban mai binciken kudi na gwamnati, ya fitar da rahoton da ke zargin cewa a shekarar 2014, kamfanin na NNPC ya ki zuba dala biliyan 16 a asusun gwamnati.

Sai dai kuma NNPC ya musanta zarge-zargen.