"Murkushe kungiyar IS ne babban burina"

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaba Obama ya ce burin gwamnatinsa ita ce ta kawar da Kungiyar IS.

Shugaba Obama ya ce samun galaba a kan kungiyar da ke ikirarin kafa daular musulunci IS, na daya daga cikin muhimman abubuwan da ya sanya gaba.

Mista Obama ya ce gwamnatinsa na iyakar kokarinta wajen gani an kawo karshen matsalar, amma ba zai yi amfani da hanyoyin da ba za su amfani kowa ba.

Ya kara da cewa, bai kamata a rika tunanin za a samu mafita ba idan aka jefa bama-bamai a Syria ko kuma Iraki, saboda hakan zai nuna rashin imanin da ka iya janyo IS ta samu karin masu ra'ayin shiga kungiyarsu.

Shugaban na Amurka ya kuma ce ba zai kyautu a nuna wa musulman Amurka kiyayya ba, wadanda a cewarsa ke da hadin kai da kishin kasarsu.