Kamfanin taxi na Uber ya zo Abuja

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Fasinjoji za su iya amfani da intanet domin neman tasi ta Uber

An kaddamar da kamfanin tasi na Uber wanda ake iya samun tasi ta hanyar intanet, a Abuja, babban birnin kasar.

Masu son amfani da motar tasin ta kamfanin Uber, za su iya yin hakan alhali suna gida ko otel, ta intanet.

Tuni dama dai kamfanin na Uber ya kaddamar da irin wannan tasin a birnin Lagos na kasar.

Sai dai kuma, a wasu biranen kasashen da ake amfani da Uber, masu tasi na haya, suna ganin Uber din na kashe musu kasuwa.