Shekau yana cikin halin takura — Masana

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shekau ya fitar da bidiyo yana aikewa da sako a karo da dama

Masana kan al'amuran da suka shafi tsaro a Najeriya, sun fara sharhi kan sabon bidiyon shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau ya fitar a ranar Alhamis.

A hirar da ya yi da BBC wani masanin sha'anin tsaro Air Commodor Abubakar Saddik Mai Ritaya, ya ce wannan bidiyo ya nuna cewa Shekau yana cikin halin takura kuma a boye.

Ya ce ya fadi haka ne duba da yadda yake bayyana a bidiyon da ya sha fitarwa a can baya, inda yake bayyana cikin walwala da kazar-kazar.

Air Commodor Saddik ya kara da cewa wannan bidiyo zai matukar karawa sojojin Najeriya kwarin gwiwa wajen ci gaba da kokarin murkushe kungiyar.

Masanin ya kuma ce duk wani kira da Shekau din ya yi a bidiyon ga magoya bayansa ba wani abu bane face kurari.

A hirar tasu da BBC, Sulaimanu Ibrahim ya fara da tambayar Air Commodor Saddik ko yana ganin ma Shekau din ne a bidiyon kuwa:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti