Sojojin Nigeria sun kwato Kala Balge

Rundunar sojin Nigeria da ke yaki da kungiyar Boko Haram a yankin arewa maso gabas, ta sanar da kwace iko da garin Kala Balge daga hannun 'yan Boko Haram.

Wata sanarwa wadda kakakin rundunar Kanal Sani Usman Kukasheka ya sanyawa hannu ta ce, yanzu dai soji sun kawar da dukkan 'yan Boko Haram da suka fake a yankin na Kala Balge.

Sanarwar ta kara da cewa, a kokarin kwace iko da garin soji sun kashe 'yan Boko Haram 22, kuma suka kawar da su daga Wumbi da Tinish da Tilem da kuma Malawaji.

Sojan Nigeriyar sun kuma ce, sun kubutar da mutane 309 da 'yan Boko Haram suka yi garkuwa da su.

Wannan dai na faruwa ne yayin da dakarun Nigeria ke ci gaba da ikirarin samun nasarar kwato garuruwa da 'yan Boko Haram suka kwace a jihar Borno.