Kamaru: An kwace magungunan fasa kwabri

Hakkin mallakar hoto SPL
Image caption fasa kwabrin magani

Jami'an tsaro da kuma na kiwon lafiya a Kamaru sun karbe magunguna a hannun 'yan fasa kwabri da nauyinsu ya kai tan uku.

An kiyasta darajar wadannan magunguna a kan kudin CFA miliyan 500.

Akasarin magungunan na dauke da tambarin kasashen Afirika ta kudu, da Brazil, da Indiya, da kuma Najeriya da babu isassun bayanai game da ingancinsu.

A karo da dama, mutanen da suke yin amfani da magungunan jabu na dinga mutuwa daga bisani.