Likitoci sun kara da bokaye a Kenya

Hakkin mallakar hoto AFP

A jerin rahotanni da ake yi kan wasiku daga Afrika, dan jarida Joseph Warunngu ya duba sa'insan da ke tsakanin Likitoci da Bokaye a Kenya.

Kamar sauran kasashen Afrika, bokaye da masu maganin gargajiya suna ko'ina a Kenya, kuma suna buga kirjin cewa suna warkar da duk cututtuka.

Zaka alamu sosai a jaridun kasar, inda bokaye kai tsaye ke tallata hajarsu da ayyukan da suke iya aiwatarwa.

Ba a jaridu kadai tallatawa ba, har ma da takardun da suke makalawa a fitilun wutan lantarkin waje.

Ba a iya kiyasta ayyukan da boka ke iya gudanarwa.

Idan dai har akwai auren da ke da matsala ko gasar kwallon kafar da ake bukatar nasarar, ko kasuwancin da ke bukatar farfadowa, toh kuwa masu maganin gargajiyar nan sun samu wajen zama daram.

Hakkin mallakar hoto AFP

A jikin tallace-tallacen ana samun kamar haka, "Mijin ki ya daina sonki? Zo ki same ni, ina da maganin da zai mallaka miki shi har abada".

Wasu kuma ke cewa, "Idan kana fama da wani mummunan ciwon da babu likitan da zai iya maka magani, to ka zo, ni zan taimake ka".

A kullum sai ka ga ire-iren wandanan tallan, kuma yawanci ba su mayar da hankali a kansu.

Hakkin mallakar hoto AFP

Ganin ma cewa bokayen na da kudaden da suke kashewa wajen talla da aka sani da tsada, ya nuna alamun harkar tasu na kasuwa.

Amma kuma yanzu masu maganin gargajiyar zasu samu kishiyoyin da suma ke da damar tallata hajarsu a jaridun da jikin fitilu, tunda Likitocin ma sun kusa samun damar tallata tasu ayyukan, sakamakon wani sauyi da aka samu a doka, wacce za a aiwatar a watan Maris.

Neman magani a kasashen waje
Hakkin mallakar hoto AFP

Ga alamu dai masu fafaren kayan na kishi ne da masu maganin gargajiyar ne, ganin cewa basu da shamaki tunda cewa suke suna maganin komai.

Ana kallon wannan yunkuri da Kungiyar Likitocin kiwon lafiya da masu kula da hakora -wanda ke sa ido kan yadda suke aiwatar da ayyukansu- suka yi, a matsayin mayar da martani.

Yanzu Likitocin zasu iya karawa da bokayen, wadanda suka mamaye kasuwar da hajar su a yayinda doka ta hana Likitoci tallata tasu basirar, da nisanta kansu.

Kungiyar Likitocin dai ta ce ba za ta bari duk wanda ba a tantace ba kuma yake bugun kirjin iya maganin wasu cututtuka, amfani da sunan Likita ba.

An kiyasta cewa, al'ummar Kenya na kashe dala miliyan 100 duk shekara domin neman lafiya a kasashen waje, musamman ma a kasar Indiya.

A halin da ake ciki dai yanzu, masu fararen kaya dauke da na'urorin duba lafiya za su shiga gasa da bokaye da masu maganin gargajiya da ke amfani da itatuwa domin kawo sauki.

Hakkin mallakar hoto AFP

Ba a san wani mataki likitocin zasu dauka wajen tallata hajar su ba, amma indai bokayen suka fi su nuna hazaka, ba wanda zai yi shakkar zuwa wajensu neman taimako.