'Turai na fuskantar barazana fiye da baya'

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Tun bayan harin da aka kai Brussels EU ta sha alwashin kawar da kungiyar IS
Jagoran Europol, wato Hukumar tabbatar da doka ta Tarayyar Turai, ya yi gargadin cewa kasashen Turai suna fuskantar barazana da ba su fuskanci irin ta ba a baya, daga mayakan kungiyar IS da ke dawowa daga Sryria.

Rob Wainright ya shaida wa BBC cewa a Turan, an cusa tsaurin ra'ayi a kan mutanen da ake zargi da suka kai 5,000.

Za su kuma iya shiga cikin kai hare-hare a kasashen Yamma, a wani bangare na sabuwar dabarar kungiyar ta IS.

Ya ce, "Babbar matsala ce da ta shafi kasashe da dama daban-daban, kuma shi ne babban abin da hukumar ta sa a gaba yanzu.

Bayan harin da aka kai ranar Talata a Brussels, ministocin kula da harkokin cikin gida da na shari'a na kasashen Tarayyar Turai za su yi taro a babban birnin Belgium din, domin tattaunawa kan yadda za'a tunkari barazanar da masu jihadi ke yi a kasashensu.