An yanke wa Karadžic hukunci

Hakkin mallakar hoto AFP Getty
Image caption Radovan Karadzic

Tsohon shugaban Sabiyawan Bosniya Radovan Karadžic zai yi zaman gidan yari na tsawon shekaru 40 bisa ga aikata laifin kisar kare dangi.

Akalla mutane 100,000 ne suka mutu a wani yakin da ya yi sanadiyar darewar Yougoslavia a cikin shekaru 1990.

Kotun shari'a manyan laifuffuka na tsohuwar kasar Yougoslavia ta ce Karadžic na da hannu a kisar Srebenica.

Alkalin kotun ya ce tsohon jagoran na masu kishin kasa ya tsugunar da wani salon siyasa domin ganin bayan musulman Bosnia.

Radovan Karadžic ya yarda da faruwar kashe-kashen rayuka , amma kuma ya ki amincewa da daukan nauyin aiwatar da haka.