Za a kafa gwamantin hadin gwiwa a Niger

Hakkin mallakar hoto
Image caption Mahamadou Issoufou shugaban Niger

Shugaban kasar Niger, Mahamadou Issoufou, ya ce a shirya ya ke ya kafa gwamnatin hadin gwiwa da 'yan adawan domin su tunkari matsalolin da ke fuskantar kasar.

A wata hira da ya yi da kamfanin dillancin labarai na AFP, Shugaba Issoufou ya ce "A shirye nake na kafa gwamnatin hadin gwiwa da 'yan adawa domin mu fuskanci barazanar da 'yan Nijar ke fama."

Shugaban ya kara da cewa akwai bukar hadin kai saboda ba matsalar tsaro ba ce kadai ke fuskantar kasar, akwai wasu kalubalen da suka shafi tattalin arziki da na zamantakewa da cigaban al'umma.

Mahamadou Issoufou dai ya samu kashi 92 cikin 100 na kuri'un da a ka kada a zabe zagaye na biyu wanda 'yan adawa suka kauracewa.

Babban abokin hamayyarsa, Hama Amadou, yana jinya a kasar Faransa a lokacin da aka yi zaben zageye na biyu.

Hukumar zaben kasar dai ta ce Amadou ya ci kaso bakwai cikin dari ne kawai na kuri'un da aka kada.