Amurka ta kashe Ministan Kudin IS

Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaba Obama na Amurka, ya lashi takwobin ganin bayan kungiyar ta IS.

Sojojin Amurka sun ce sun kashe wani babban dan kungiyar IS, wanda ake yiwa lakabi da ministan kudi a kungiyar.

Sakataren tsaro na Amurka, Ashton Carter ya kira shi da Haji Imam, amma sunansa na gaskiya shine Abd Rahman Mustafa Al Qaduli.

Sai dai babu wani bayanin game da yadda Amurkan ta hallaka shi, ko kuma a inda ta hallaka shin.

Kazalika Mista Carter ya ce sojojin na Amurka na hallaka wasu da ya kira jagororin kungiyar daya bayan daya.

A farkon watannan Maris ne, Hedikwatar tsaron Amurkan, watau Pentagon ta ce ta kashe wani kwamanda wanda kungiyar ta yiwa lakabi da ministan yaki.