Nigeria: An kashe 'yar kunar bakin wake

Hakkin mallakar hoto Nigeria Army
Image caption Rundunar sojin Najeriya ta kara matsa kaimi wajen ganin ta kawo karshen Boko Haram a kasar.

Dakarun sojin Najeriya sun gano wasu mata biyu da ake zargi 'yan kunar bakin wake ne a unguwar Molai da ke kauyen Umurari, a kudancin birnin Maiduguri, arewa maso gabashin kasar.

A wata sanarwa da rundunar sojin Najeriyar ta fitar, ta ce dakarunta sun gano matan ne da taimakon 'yan kato da garo, wadanda aka fi sani da Civilian JTF ne wuraren karfe daya na dare.

Wani dan JTF din mai suna Babakura Kolo, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa, "Lokacin da 'yan kato da goran suka haska wa matan fitila, dai neman sanin ko su wanene, sai daya cikin su ta fashe nata bam din, yayin da dayar kuma sai ta tsere ta shige wannan kango".

Ya kara da cewa, daga bisani sai sojoji suka bi ta ciki suka kuma harbe ta da suka ga tana neman fashe nata bam din.

An sha samun ire-iren harin na kunar bakin wake a garin na Molai, wanda ke da nisan kilomita 6 daga Maiduguri, inda ranar 16 ga watan Maris wasu mata biyu 'yan kunar bakin waken da suka yi shigar maza, suka kashe mutane 25, yayinda mutane 32 suka jikkata a wani hari da suka kai masallacin garin.

Kakakin rudunar sojojin Najeriyar Kanal Sani Kukasheka Usman, ya ce hanakli ya kwanta a garin, kuma jama'a na cigaba da gudanar da harkokin yau da kullun.