'Yan sanda na diran mikiya a Brussels

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption A ranar Alhamis, 'yan sandan Belgium din suka kama mutane 6 a Brussels.

'Yan sanda a Brussels sun harbe, tare da raunatawasu mutane biyu a wani samame da suka kai a Brussels.

Masu shigar da kara sun ce mutanen na cikin wasu guda uku da aka tsare ranar Jumma'a, bayan harin da aka kai birnin.

Hotunan bidiyo da aka gano a yankin Schaerbeek ya nuna jami'an tsaro da manyan bindigogi suna afkawa wani mutumi da alamu ke nuna ya samu rauni kusa da wani wajen aje keken kayayyaki, kafin daga bisani suka janye da kafafuwansa.

Jami'an tsaron sun ci gaba da kame a kasashen Faransa da Jamus.

Shugaban Faransar Francois Hollande ya ce ana kokarin kakkabe kungiyar 'yan ta'addan da ke da alhakin hare-haren da aka kai birnin Paris da Brussels din, amma ya yi gargadn cewa mai yiwa ba za a rasa sauran wasu ba.

A baya dai kafofin yada labarai na kasar Belgium sun ce 'yan sanda sun hana wani mutun aikata abin da yayi niyya, lokacin wani samame da suka kai a gundumar Sharbik, a Brussels.

Kafafen yada labaran sun ce an ji karar fashewar wani abu lokacin samamen.

Samamen na baya-bayan nan ya zo ne kwanaki uku da kai hare-hare a filin jirgin sama da kuma wata tashar jirgin kasa a Brussels din, wadanda suka yi sanadiyyar mutuwar mutane 31, da raunata wasu da dama.