An kama 'yan kunar bakin wake a Kamaru

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption jami'an tsaro na Kamaru

Jami'an tsaro a Kamaru sun tabbatar da kama wasu 'yan mata 2 'yan kunar bakin wake a yau a garin Limani mai iyaka da Najeriya.

'Yan matan na hannun jami'an tsaro a garin Mora inda ake ci gaba da yi musu tambayoyi.

Sai dai kuma mai magana da yawun ma'aikatar tsaro Kanar Didier Badjeck ya musanta cewa 'yan matan 'yan Chibok ne.

Amfani da kananan jirage marasa matuka da jami'an tsaro na BIR suke yi, na ci gaba da taimaka wajen gano Boko Haram daga nesa.