An gano wanda ya kashe dalibi a Masar

'Yan sanda a Masar Hakkin mallakar hoto
Image caption An gano gawar dalibin kwanaki tara da sace shi a cikin wani rami.

'Yan sanda a kasar Masar, sun ce sun gano wanda ya kashe dalibin nan dan kasar Italia Giulio Regeni, da aka tsinci gawarsa a wani rami a birnin Alkhahira a watanni biyu da suka wuce.

'Yan sandan sun ce sun tsinci jakar dalibin, a wurin wasu gungun masu aikata muggan laifuka a wata musayar wuta da suka yi da jami'an tsaro.

Sun kara da cewa kungiyar masu aikata muggan laifukan sun yi su na wajen sace baki 'yan kasar waje a kasar, inda suke yin sojan gona a zuwan jami'an 'yan sanda ne.

A watan Junairu ne aka nemi Giulio Regeni aka rasa, bayan kwanati tara kuma ka tsinci gawarsa an jefa wani rami.