Amurka na zargin 'yan Iran da satar bayanai

Satar bayanan Sirri Hakkin mallakar hoto
Image caption Ma'aikatar shari'ar Amurka ta ce mutanen na yi wa kasar su aiki ne.

Amurka na zargin wasu Iraniyawa bakwai da yunkurin satar bayanan sirrin kusan Kamfanoni 50 da na kasar.

Mutanen da ake zargi Ahmad Fathi, da Hamid Firoozi, da Amin Shokoli, da Sadegh Ahmadzadegan da Omid Ghaffarinia, da Sina Keissar da kuma Nader Seidi dukkan su 'yan asalin Iran ne.

An yi kokarin satar bayanan ne tsakanin shekarar 2011 zuwa 2013, wanda aka yi amanna da cewa Kamfanonin Iran ne suka shirya su.

Ma'aikatar shari'ar Amurka ta samu mutanen bakwai da laifin, wanda ake zaton su na yi wa gwamnatin Iran aiki daga wajen kasar.

Ma'aikatar ta kira su da wadanda suka kware akan na'ura mai kwakwalwa, ya yin da jami'an Amurka suka ce wannan yunkuri kamar sako ne da ke nuna ya kamata a kara daukar matakai akan masu kutse dan satar bayanan sirri a kasar.

Wannan dai shi ne karon farko da Amurka ke tuhumar 'yan kasar waje da yi wa gwamnatin su aikin satar bayanan sirri a ma'aikatar kudi da Ruwa da kuma ma'aikatar da ke kula da ayyukan ababen more rayuwa.

Babbar mai shigar da karar gwamnatin Amurka Loretta Lynch ta ce hakan babbar barazana ce ga tattalin ariziki da tsaron kasar.