Mawakan Ivory Coast sun kalubalanci Al-Qaeda

Hakkin mallakar hoto
Image caption A farkon watan Maris ne kungiyar Al-Qaeda ta kai hari otal din Grand Bassam da ke Ivory Coast
Mawakan kasar Ivory Coast sun saki wata sabuwar waka ta hadin gwiwa inda suka mayarwa mayakan Al-Qaeda martani cewa ba sa tsoronsu, bayan harin da kungiyar ta kai wanda ya kashe mutane 19.

Kungiyar Al-Qaeda ce ta dauki alhakin harin da aka kai otal din Grand Bassam da ke bakin teku a farkon watan nan.

An dauki bidiyon wakar ce mai taken "Meme Pas Peur", "babu tsoro ko kadan", a tekun na Grand Bassam, inda a can ne 'yan bindigar suka bude wuta.

Wakar wadda aka yi ta da Faransanci ta kunshi maganganu da dama da suka hada da cewa mayakan, "Kun kashe wadanda ba su ji ba ba su gani ba, don haka ba zaku shiga aljanna ba."

Kazalika a cikin wakar mawakan sun ce, "Mu 'yan Ivory Coast tsaye mu ke a kan kafafunmu."

Wanda ya shirya wakar Chico Lacoste, ya shaida wa BBC cewa sun yanke shawarar yin wakar ne don sh gayawa duniya cewa, "Duk da cewa an kai hari Ivory Coast to haka ba zai taba kassara mu ba."

A kasar Ivory Coast abu ne da ya zama jiki yin waka don mayar da martani kan duk wani abu da ya faru na rikici ko na neman sasantawa.

Karin bayani