Auren mu da Sadiya raha ce —Baballe

Hakkin mallakar hoto baballe

Fittaccen jarumin fina-finan Hausa, Baballe Hayatu, ya musanta rahotannin da ake yada wa cewa an daura aurensa da Sadiya Gyale.

A hirar da ya yi da BBC, Baballe ya ce wani abokin aikinsa ne a Kannywood ya kirkiri labarin, ya kuma sa shi a shafukan sada zumunta da muharawa wanda kuma ya yadu kamar wutar daji.

Jarumin ya ci gaba da cewa sakamakon wannan labari har Ali Nuhu ya yi fushi da shi ganin cewa suna tare amma bai sanar da shi daurin auren ba.

Ya kuma kara da cewa Sadiya ta tafi umara a Saudiyya ba ta kuma san da labarin ba, ya kuma ce babu maganar aure a tsakaninsu sai dai mutunci.

Ga hirar su da Yakubu Liman ta wayar tarho.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti