Gobara ta tashi a babbar kasuwar Kebbi

Image caption "Gobarar ta kone kusan rabin kasuwar, an kuma yi hasara ta miliyoyin naira", a cewar wani mazaunin garin

Wata gobara ta tashi a babbar kasuwar Kebbi da ke arewacin Najeriya a daren Juma'a.

A wata hira da BBC ta yi da wani mazaunin garin ya ce gobarar ta tashi ne da dare kuma har wayewar gari na Asabar ba a samu sa'ar kashe ta ba.

Ba a san abin da ya haddasa gobarar ba, sai dai ya ce wutar ta kone kimanin kashi 80 na kasuwar.

Kawo yanzu babu labarin rasa rayuka ko jikkata, sai dai an yi hasarar dukiya ta miliyoyin nairori.

Image caption Wasu daga cikin rumfunan kasuwar da suka kone