An zabi sabon kakakin Majalisa a Nijar

Muhammadou Issoufou
Image caption 'Yan adawa sun kauracewa zaben kakakin majalisar.

A jamhuriyar Nijar an zabi honorable Usaini Tinni na jam'iyar PNDS Tarayya a mukamin shugaban majalisar dokokin kasar.

Yan majalisar na bangaren masu rinjaye ne kadai suka zabe shi kasancewar yan adawa na ci gaba da kaurace ma zaman,inda ya samu kuri'u 109 daga cikin kuri'u 118 da aka kada.

A ranar talata mai zuwa ne idan Allah ya yarda kotun tsarin mulkin kasar za ta rantsar da shi.