Niger: 'Yan adawa sun kauracewa zaman majalisa

Hakkin mallakar hoto AFP Getty
Image caption Hama Amadou shi ne dan takarar jam'iyyar da ta fadi zaben shugaban kasa na Nijar
'Yan adawar jamhuriyar Nijar sun ce sun dauki matakin kaurace wa zaman majalisar dokokin kasar har nan da 'yan kwanaki domin nuna rashin amincewarsu da zaben da ya gabata.

Sun kuma ce in har shugaba Issoufou na son kafa gwamnatin hadin kan kasa to wajibi ne a zauna a duba lamarin zaben.

A nasu bangaten kuwa masu rinjaye a zaben na ganin bakin alkalami ya riga ya bushe.

Honorabul Murtala Alhaji Mamuda na jam'iyar MNSD Nasara ya shaida wa BBC cewa, hujjojinsu na kaurace wa majalisar sun hada, kura-kuran da aka tafka a zaben

Ya kara da cewa ba za su janye kudurinsu ba har sai masu sa ido kan zabe na duniya da na cikin gida sun zo an zauna kan teburi an baje abubuwa yadda suka dace.

Su kuwa a bangaren 'yan majalisar jam'iyya mai ci cewa suka yi wannan lamari ba sabon abu bane, kuma suna da yakinin bangaren adawar za su janye aniyar tasu nan ba da jimawa ba.niger opposition