'Kamfanoni 300 sun ci kudi a Nigeria'

Image caption Fadar shugaban kasar ta ce an samu dawo wa gwamnati da dala miliyan 35, yayin da ake sa ran a dawo da wasu karin kudaden da suka kai dala miliyan 200.

Fadar shugaban Najeriya ta ce an samu wasu kamfanoni, da wasu sanannun mutane a kasar da laifi, bayan binciken da aka gudanar kan kwangilolin da ofishin mai bai wa shugaban kasar shawara kan sha'anin tsaro ya bayar a can baya.

Cikin wadanda ake zargi, akwai manyan jami'an soji masu aiki yanzu, da wadanda suka yi ritaya.

A wata sanarwa da ta fito daga fadar shugaban kasa, ta ce, kwamitin ya samu manyan mutane da suka hada da jami'an soji masu ci da wadanda suka yi ritaya da hannu a badakalar.

Sanarwar ta ce zuwa yanzu an karbo naira biliyan bakwai daga kamfanoni da kuma mutanen da aka samu da laifin na kwangilar fiye da shekaru hudu.

A nan gaba ne kuma za a kara karbo naira biliyan 41 daga hannun wasu kamfanonin da mutane.

Tuni dai aka bai wa hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa EFCC, umarnin ci gaba da bincike don gano ko za a sake karbo wasu kudaden kimanin naira biliyan 75 daga hannun wasu kamfanonin na kwangilolin da aka basu amma basu kammala ba.

Sanarwar ta ce kwamitin ya gano cewa an biya daya daga cikin kamfanonin Societe D'Equipment International, kudaden da suka fi yawan na kwangilar da aka bashi da kimanin dala miliyan 7.09.

Shugaba Buhari ya sha alwashin yaki da cin hanci da rashawa wanda ya yi wa Najeriya dabaibayi, kuma tun bayan kama mulki ake ta gurfanar da jami'ai da mutanen da ake zargi da sama da fadi da kudaden talakawa.