An kashe dan Polio a Afghanistan

polio a afghanistan Hakkin mallakar hoto MOH
Image caption Cutar Polio a kasashen Afghanistan da Pakistan ta zama annoba

An kashe wani jami'in lafiya mai kula da allurar Polio a Afghanistan a yankin wasu kabilu kusa da bakin iyaka.

Jami'in mai suna Akhtar Khan na zaune ne a dakin shan maganin da ya ke aiki, yayin da wasu 'yan bindiga suka bude mi shi wuta.

Masu da'awar musulunci dauke da makamai a kasar na zargin cewa alluran riga kafi wani shiri ne na hana 'ya 'yansu haihuwa.

Kasashen Afghanistan da Pakistan sune kasashe biyu da suka rage inda cutar Polio ta zama annoba.