Gobarar sabongari
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Gobarar Sabon Gari a Kano ta ci gaba

A hirar da BBC ta yi da Sakataren kungiyar 'yan kasuwa jihar Kano KASTU Auwalu Gabari Jakada ya ce, har yanzu wutar ba ta mutu ba, da ta lafa sai ta sake tashi.

Sannan ya kara da cewa motocin kashe gobara na kamfanoni sun kawo gudunmawa a kokarin da ake yi na kashe wutar.

'Yan kasuwa na ta kokarin kwashe kayansu a inda gobara ba ta kai ba.

Da daren Juma'a ne gobarar ta tashi, ba a kuma san abinda ya haddasa ta ba.