An shawo kan gobarar Sabon Gari

Gobarar da ta tashi a kasuwar Sabon Gari a Kano ta fara lafawa.

Wakilin BBC da ke wurin ya ce, jami'an kashe gobara sun fara cin nasarar rage karfin ta.

Ya kuma kar da cewa "hayakin da yake tashi sakamakon gobarar ya fara raguwa".

A wani mataki na nuna alhini, kungiyar yan kasuwar kwanar Singa mai makwabtaka da kasuwar Sabon Garin ta umarci 'ya 'yanta da kada su bude shaguna ko kasa kayayyaki.

Ga hoton bidiyon da wakilinmu Yusuf Ibrahim Yakasai ya aiko mana.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti