Nigeria: Mutane 3 sun mutu a rikicin Ibi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jami'an tsaro basu ce komai ba tukun game da lamarin, duk da cewar an baza tsaro a garin na Taraba.

Rahotanni daga garin Ibi dake jihar Taraba na cewa akalla mutane 3 sun rasa rayukansu, wasu kimanin 12 kuma suka jikkata, sakamakon wani tashin hankali da ranar Juma'a.

An dai kai wadanda lamarin ya rutsa da zu zuwa asibiti domin jinya.

Wannan tashin hankali dai ya barke ne yayin da al’ummar musulmi ke zuwa Masallaci, domin Sallar Juma’a, inda musulmin suka yi zargin cewa wasu wadanda ba musulmi ba sun takale su, suna masu kalamai na batanci suka kuma bude masu wuta da bindiga.

To sai dai kuma, al’ummar kirista na musanta cewa su ne suka fara takalar musulmin masu zuwa sallar Jumma’a, suna zargin cewa lamarin ya taso ne yayin da wasu musulmin dake zuwa sallah a kan babur suka tsokani mata wadanda ba musulmi ba.

Ya zuwa yanzu dai jami'ai basu tanka ba game da lamarin, sai dai rahotanni na cewa an baza jami’an tsaro a garin na Ibi, wanda ya sha fama da rigingimu masu nasaba da kabilanci da addini.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ga rahoton da wakilinmu Ishaq Khalid ya aiko mana daga Bauchi.