Uganda: An zartar da dokar riga kafi

Hakkin mallakar hoto

A Uganda an zartar da wata doka da ta tilastawa iyaye tabbatar da cewa, sun yi wa yaransu alluran riga kafin wasu cututtuka.

Iyaye zasu iya fuskantar daurin da ya kai na wata shida idan ba su ba su bi dokar ba.

Dokar kuma ta bukaci yara su zama suna da katin riga kafi da zai ba su damar zuwa makaranta.

Ministar kiwon lafiya matakin farko, Sarah Achieng Opendi ta fadawa BBC cewar, kashi uku cikin 100 na yara ba a musu riga kafi ba saboda wasu kungiyoyin wasu addinai ba su yarda da yiwa yaransu riga kafi ba.

Makonni biyu da suka gabata ne dai shugaba Yoweri Museveni ya sanya hannu akan dokar ta tilasta yin riga kafi.