'Yan fansho sun koka kan rashin albashi a Bauchi

Hakkin mallakar hoto Bauchi State Govt
Image caption Gwamnan jihar Bauchi ya ce duk wanda aka tabbatar ma'aikaci ne na hakika zai samu hakkin sa

A jihar Bauchi da ke arewacin Najeriya rahotanni sun ce dubban ma'aikata da 'yan fansho sun fada cikin wani mawuyacin hali, saboda yadda hukumomi su ka yi kuskuren sanya sunayen su cikin rukunin ma'aikatan boge.

Ma'aikatan da lamarin ya shafa dai ba su samu albashin su, kana 'yan fansho ma ba su samu kudaden su na fansho ba, sanadiyar matsalar.

A wata hira da BBC, shugaban kungiyar 'yan fansho a jihar ya ce suna goyon bayan matakin tatantace ma'aikata amma sun bukaci gwamnati da ta inganta tsarin tantance ma'aikatan don sauwake wahalhalun da ma'aikata da 'yan fansho ke fuskanta.

To sai dai kuma gwamnatin jihar ta ce tana daukar matakai domin gyara kuskuren kuma duk wanda aka tabbatar ma'aikaci ne na hakika zai samu hakkin sa.