Brussels:An tuhumi wani mutum da ta'addanci

Hakkin mallakar hoto Reuters

Masu gabatar da kara a Belgium wadanda ke binciken harin kunar bakin wake da aka kai Brussels a ranar Talata sun tuhumi wani mutum da ake zargi da aikata kisan ta'addanci.

An baiyana sunan mutumin a matsayin Faycal C.

An tsare shi a ranar Alhamis a wajen ofishin masu binciken a Brussels.

An gudanar da bincike a gida sai dai ba a sami makamai ba.

Masu gabatar da karar ba su tabbatar da rahotannin kafofin yada labarai ba da ke cewa Faycal C shi ne mutumin da kamarorin tsaro suka dauki hotunansa sanye da malafa da riga jacket mnai ruwan toka tare da wasu mutane biyu da ake zargi sauran maharan ne.

Haka kuma an tumi wani mutumin mai suna Abubakar A da shiga cikin ayyukan kungiyar yan ta'adda.