Chadi : Wasu sun nemi dauri a gidan yari

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Barikin jami'an tsaro a N'Djamena

Wasu mutane 12 magoya bayan kungiyoyin fararen hula, sun kai kansu gidan yarin birnin N'Djamena ranar asabar, inda suka bukaci a dauresu.

Sun yi haka ne domin nuna fushi da kuma kauna ga shugabanninsu hudu da aka kama ranar Alhamis.

Zaman neman sasantawa da aka yi tsakanin Gwamnati da kungiyoyin fararen hula ya ci tura, a dalilin rashin jituwa game da wasu sharruda.

Wannan lamari ya faru ne a lokacin da ake yakin neman zaben shugaban kasar wanda za a yi a ranar 10 ga watan Afrilu.