An kama mutumin da ya ari kaset tun shekaru 14 bai mayar ba.

Image caption James Meyers ya ari kaset shekaru 14 bai mayar ba.

An kama wani mutum mazaunin Arewacin Carolina a Amurka saboda kin mayar da Kaset din da ya ara shekaru goma sha hudu da suka gabata.

Mutumin mai suna James Meyers ya ce ya na zaune a cikin motarsa kawai sai ga jami'an tsaro suka ce an ba su takardar izinin kama shi.

A shekarar 2002 ne dai Mr Meyers ya je wani shagon bada hayar Kaset na J&J ya ari Kaset din barkwanci, kuma tuni aka rufe shagon.

An gurfanar da shi gaban kotu, amma tun kafin a fara shar'ar aka sallame shi, bayan ya biya tarar dala 200.

Mr. Meyers ya ce wannan ne karon farko da aka fara saka masa ankwa a hannu.