Sojojin Syria na fafatawa a Palmyra

Hakkin mallakar hoto AFP

Ana ci gaba da fafatawa tsakanin sojojin gwamnatin Syria da mayakan IS a ciki da wajen Palmyra daya daga cikin mashahuran wuraren tarihi a Gabas Ta Tsakiya.

Rahotanni na cewa sojojin Syria da ke samun goyon bayan jiragen yakin Rasha da kuma nayaka masu marawa gwamnatin baya suna kokarin shiga garin ta fuskoki da dama.

A bara ne dai yan IS suka kwace garin na Palmyra.

Hotunan bidiyo sun nuna hayaki ya turnuke sararin samaniya yayin da tankokin sojin ke ci gaba da yin luguden wuta a birnin.