An samu bullar cutar Zika a Chile

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ma'aikatar lafiya a Chile ta ce an samu wadda ke dauke da cutar Zika a kasar.

Jami'an lafiya a Chile sun rawaito cewa an samu bullar cutar Zika a kasar.

Ma'aikatar lafiya ta kasar ta ce wata mata ce ta kamu da cutar sakamakon jima'i da ta yi da wani mutum a Haiti.

Cutar ta Zika wadda sauro ke yada ta ba bu ita a Chile, hakan yasa wannan ne karon farko da aka samu wanda ke dauke da ita.

Cutar wadda ta yadu a Latin Amurka ana dangantata da haifar da tawaya ga jarirai.

Kazalika cutar na janyo nakasa ga jarrirai musamman haifar da matsala a kwakwalwar su.

Masu bincike sun ce sun gano yadda kwayar cutar Zika ka iya lalata kwayoyin halittar da ke cikin kwakwalwar 'yan tayi.

Wani sabon bincike ya gano cewa cutar Zika za ta iya haddasa mummunar rashin lafiyar da ke shafar jijiyoyin jiki, wadda a karshe ka iya zama sanadin shanyewar jiki.